Kakakin Majalisa: Onyejeocha da Odebunmi sun janye wa Gbajabiamila takara

Kakakin Majalisa: Onyejeocha da Odebunmi sun janye wa Gbajabiamila takara

Wani rahoto da jaridar Vanguard ta ruwaito ya haskaka cewa, wasu manyan 'yan takara biyu, Segun Odebunmi da kuma Nkeiruka Onyejeocha, a ranar Lahadi sun janyewa Femi Gbajabiamila takarar kujerar kakakin majalisar wakilai.

Jagoran kungiyar yakin neman zaben Gbajabiamila, Honarabul Abdulmumin Jibrin, shi ne ya bayar da wannan sanarwa a taron 'yan majalisa gabanin zaben manyan shugabannin majalisar da za a gudanar a ranar Talata 11, ga watan Yunin 2019.

Sai dai a yayin bayar da wannan sanarwa, daya daga cikin manyan 'yan takarar biyu da suka yi amai suka lashe na janye kudiri, Nkeiruka Onyejeocha, ba ta halarci taron 'yan majalisar da aka gudanar ba a ranar Lahadi.

Honarabul Jibril ya kuma bayar da sanarwar sunayen 'yan majalisar da suka janye takarar su ta kujerar kakakin majalisa tun makonni hudu da suka gabata.

KARANTA KUMA: A yi taka tsan-tsan a kan Sarki Sanusi - Yayale ya gargadi gwamnatin Kano

A halin yanzu dai jam'iyyu kimanin 35 sun shimfida goyon bayan su a kan takarar Honarabul Femi Gbajabiamila domin tabbatar da nasarar sa ta lashe kujerar kakakin sabuwar majalisar wakilai ta tara a tarihin dimokuradiyyar kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel