Jastis Garba ya maye gurbin Bulkachuwa a kotun daukaka karar zaben shugaban kasa

Jastis Garba ya maye gurbin Bulkachuwa a kotun daukaka karar zaben shugaban kasa

Kamar yadda jaridar The Punch ta bayar da shaida a yanzu din nan Justice M.L Garba, shi ne sabon shugaban kotun daukaka karar zaben shugaban kasa na Najeriya a yayin da ya kasance shugaban kotun daukaka kara reshen jihar Legas.

Justice Garba wanda ya kasance cikin jerin manyan alkalai na kasa da hukumar shari'ar kasar nan ta nada a ranar Litinin, ya maye gurbin tsohuwar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya, Justice Zainab Bulkachuwa.

Bulkachuwa ta zame hannun ta daga jagorancin kotun sauraron korafe korafen zaben shugaban kasa a ranar 22 ga watan Mayun da ta gabata biyo bayan zargin ta da yiwuwar nuna wariya ga jam'iyyar adawa ta PDP da kuma dan takarar ta na zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu, Atiku Abubakar.

Jam'iyyar PDP tare da tsohon mataimakin shugaban kasa na ci gaba da kalubalantar sakamakon babban zaben kasa da hukumar INEC ta tabbatar da nasarar Shugaba Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyar sa ta APC.

KARANTA KUMA: Gwamnatin ka ta tsarkaka da duk wanda lambar su ta fito a hannun EFCC - ARDI ta roki Buhari

Ko shakka babu Justice Zainab wadda ta yi zurfin gaske a ilimin shari'a tun ba ta wuce shekaru 40 ba kuma haifaffiyar jihar Gombe, ta kasance mace ta farko da ta rike wannan mukami na shugabar kotun daukaka kara a kasar Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel