Babu ma'alukin da zai iya hana Buhari sake nada ni minista - Solomon Dalung

Babu ma'alukin da zai iya hana Buhari sake nada ni minista - Solomon Dalung

Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya hana shugaba Muhammadu Buhari sake nadashi minista a wannan sabuwar gwamnatin da aka shiga.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar kan rikicin da ya wakana a kungiyoyin wasannin kwallon kafa, tseren gudu da kwallon kwando lokacin da yake mulki.

Yayinda aka bukaci fashin baki kan zargin cewa wasu masu ruwa da tsaki dake kokarin hana shugaba Buhari sake nadashi, yace: "Babu wanda ya isa ya hana nadani idan Allah ya nufa. Bana tayar da hankali kan jita-jita."

"Ubangiji ke bayar da mulki, idan ya sake bani mulki, zan mayar da hankali kan kawo cigaba wajen gina tushe, zan yi amfani da mafi yawan kudin gwamnati wajen yin hakan."

Kwanaki 11 kenan da fara wa'adin shugaba Buhari na biyu amma babu ministocin da zasu tayasa aiki. Hakazalika har yanzu bai yi wani muhimmin nadi ba a fadar shugaban kasa.

Alkaluma sun nuna cewa shugaba Buhar na rike da takardan sabbin ministocinsa a hannu kuma bai bayyanata ga kowa ba. Kawo tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ne aka tabbatar da cewa ba zai dawo ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel