Zarra: Ekweremadu, Dino Melaye, Sanatocin PDP 35 sun lamincewa Ahmad Lawan

Zarra: Ekweremadu, Dino Melaye, Sanatocin PDP 35 sun lamincewa Ahmad Lawan

Da alamun dan takaran kujeran shugabancin majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, zai lashe zaben gobe yayinda Akalla sanatocin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP 37 suka bayyana goyon bayansu gareshi

Wannan ya biyo bayan abinda ya faru ranar Asabar inda sabbin sanatocin jam'iyyar All Progressives Congress APC suka alanta goyon bayansu garesu. A yanzu, sanata Ahmad Lawan na da kuri'u 99.

Hakan ya sanya babban abokin hamayyarsa, Sanata Ali Ndume, cikin tsaka mai wuya inda sanatoci goma kacal suka rage masa cikin 109.

A gobe, 11 ga watan Yuni za'a gudanar da zaben sabuwar majalisa ta tara.

Ahmad Lawan, Ndume, da Danjuma Goje, dukkansu yan yankin Arewa maso gabashin Najeriya suke takarar kujerar shugaban majalisar dokokin tarayya amma Goje ya janye daga baya bayan ganawarsa da Buhari.

Saboda tabbatar da rinjayensa, Lawan ya gana da sanatocin PDP 37 a ranar Asabar.

Wannan ganawa ya gudana ne a gidan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu a Abuja.

Daga cikin sanatocin da suka halarta sune, Eyinnaya Abaribe, Emmanuel Bwacha, Dino Melaye, Theordore Orji, Philip Aduda, da James Manager.

A bangare guda, Sanata Ali Ndume ya lashi takobin cewa babu gudu, babu ja da baya, babu ma'alukin zai iya sanyashi janyewa daga wannan takara da za'a ranar Talata

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel