Dasuki: Ana so a ladabtar da tsohon Ministan Najeriya Malami

Dasuki: Ana so a ladabtar da tsohon Ministan Najeriya Malami

Labari ya kawo gare mu cewa a Ranar Alhamis dinnan, 13 ga Watan Yuni, 2019, ne tsohon Ministan shari’a na Najeriya watau Malam Abubakar Malami SAN zai fuskanci wani kwamitin bincike.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kwamitin da ke da alhakin ladabtar da Ma’aikatan shari’a ta gayyaci Abubakar Malami wanda yayi aiki a matsayin Ministan shari’a a gwamnatin shugaba Buhari.

Kamar yadda mu ka samu labari, wannan kwamiti ya gayyaci tsohon Ministan ne bayan korafin da Iyalin Kanal Samo Dasuki (mai ritaya) su ka rika aikawa zuwa gaban kungiyar NBA ta Lauyoyin kasar nan.

Iyalin tsohon mai ba shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, su na karar Abubakar Malami ne bayan wasu kalamai da yayi a gidan jarida a matsayin hujjar gwamnati na tsare Dasuki.

KU KARANTA: Buratai da Takwarorinsa za su cigaba da zama a ofis bayan shekaru 4

Gwamnatin Najeriya ta ki sakin tsohon NSA Sambo Dasuki duk da umarnin da kotu su ka bada na cewa a bada belinsa. Malami a lokacin yana Minista, ya tubure yace laifin da ke kan Dasuki, ba zai bari a kyale sa ba.

Malami yake cewa Kanal Sambo Dasuki yana da hannu wajen mutuwar mutane fiye da 100, 000 a Najeriya a lokacin Jonathan, don haka bai dace a kyale sa ya kubcewa hukuma saboda wani umarnin kotu ba.

Wannan ya sa Iyalin tsohon jami’in na gwamnatin Jonathan su ke so kungiyar ta hukunta Abubakar Malami da laifin sabawa dokar aiki da kuma taka dokokin kasa da tsarin mulkin Najeriya a lokacin yana ofis.

Mai dakin Kanal Sambo Dasuki watau Hajia Bintu Sambo Dasuki; da kuma ‘Dan sa, Abubakar Atiku Dasuki da ‘yan uwansa irin su Sanata Umar Dahiru, ne su ka rubuta wannan korafi gaban kungiyar NBA ta Lauyoyi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel