Gwamnatin ka ta tsarkaka da duk wanda lambar su ta fito a hannun EFCC - ARDI ta roki Buhari

Gwamnatin ka ta tsarkaka da duk wanda lambar su ta fito a hannun EFCC - ARDI ta roki Buhari

Biyo bayan rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayun 2019, ana ci gaba da kirdadon sunayen wadanda sabuwar majalisar sa za ta kunsa na ministoci da kuma manyan mukamai na fadar sa.

Wata cibiyar bincike a kan harkokin da suka shafi yaki da rashawa ARDI (Anti-Corruption and Research Based Data Initiative), ta shawarci shugaban kasa Buhari a kan wadanda sabuwar majalisar ya dace ta kunsa.

Cibiyar ARDI ta shawarci shugaban kasa Buhari a kan ya tabbatar da gwamnatin sa ta tsarkaka daga duk wanda lambar sa ta fito a hannun hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC ba tare da ta wanke shi ba.

Yayin mika kokon ta na bara, ARDI ta ce kada sabuwar majalisar Buhari ta kunshi duk wani mai kashi-a-jika da zargin aikata laifukan rashawa ba tare da hukumomi masu yaki da rashawa sun tsarkake shi ba.

KARANTA KUMA: Makiyaya sun salwantar da rayukan mutane 3,641 a Najeriya - WAANSA

Babban sakataren cibiyar ARDI, Dennis Aghanya, shi ne ya jaddada muhimmancin hakan cikin garin Abuja a ranar Lahadin da ta gabata. Ya ce akwai bukatar sabuwar gwamnatin Buhari ta sanya shamaki na haramtawa mabarnata rikon madafan iko.

Ana iya tuna cewa, binciken cibiyar ARDI ne ya yi sanadiyar shigar da karar tare da tsige tsohon alkalin alkalai na kasa, Jastis Samuel Walter Onnoghen da a halin yanzu shugaba Buhari ya amince da takardar sa ta murabus.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel