Makiyaya sun salwantar da rayukan mutane 3,641 a Najeriya - WAANSA

Makiyaya sun salwantar da rayukan mutane 3,641 a Najeriya - WAANSA

Babu shakka aukuwar rikicin makiyaya da manoma ta bar baya da kura a kasar nan sakamakon asarar dumbin rayuka da kuma dukiya da ta haifar cikin tsawon shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata kawo wa yanzu.

Kimanin rayukan mutane 3,641 sun salwanta yayin aukuwar hare haren makiyaya a tsakanin watan Janairu na shekarar 2016 zuwa watan Oktoba na shekarar 2018. Wannan asarar rayuka ta auku cikin jihohin Benuwai, Taraba, Kaduna, Zamfara, Filato da kuma Nasarawa.

Josephine Habba, shugabar cibiyar kula da shige da fice kananan makamai a yankin Yammacin Afirka, WAANSA, ita ce ta bayar da shaidar hakan a ranar Lahadin da ta gabata cikin birnin Makurdi ne jihar Benuwai.

A yayin taron tunawa da makon wannan shekara na kula da shige da ficen makamai da aka gudanar a yankin Arewa ta Tsakiya, Josephine ta ce aukuwar hare-haren makiyaya cikin tsawon wannan lokaci ya salwantar da muhallan kimanin mutane 483,692 a jihar Benuwai kadai.

Josephine ta ce wannan kididdiga ta alkalumma ta yi daidai da binciken da gidauniyar JDF, Jireh Doo Foundation ta gudanar a sansanan 'yan gudun hijira na jihar Benuwai tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar.

KARANTA KUMA: Ya kamata a samar da dokar yaye bambanci tsakanin Mata da Maza a fagen aiki - Dangote

A cewar ta, cikin tsawon wannan lokaci na shekaru biyu, bayan garkuwa da mutane 73, rayukan mutane 411 sun salwanta a Arewa maso Gabashin Najeriya yayin da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta zartar da hare-hare 65.

Jogarar cibiyar WAANSA ta ce a yayin da kimanin mutane miliyan 5.2 ke da bukatar tallafin abinci a yankin Arewa maso Gabas kamar yadda majalisar dinkin duniya ta tabbatar, a halin yanzu akwai kimanin mutane miliyan 1.7 dake sansanan 'yan gudun hijira cikin jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel