Tambuwal ya halarci jana’izar mutane 25 da yan bindiga suka kashe a Sakkwato

Tambuwal ya halarci jana’izar mutane 25 da yan bindiga suka kashe a Sakkwato

Gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya halarci jana’izar wasu mutane 25 da yan bindiga suka kashesu a wani hari da suka kaddamar a wasu kauyuka uku cikin karamar hukumar Rabah, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kammala jana’izar keda wuya, sai gwamnan tare da sarakunan gargajiya, shuwagabannin hukumomin tsaro da manyan jami’an gwamnatinsa suka rankaya zuwa zuwa gidajen iyalan mamatan don jajanta musu.

KU KARANTA: Buhari ya yi maraba da murabus din Alkalin Alkalai Onnoghen

Tambuwal ya halarci jana’izar mutane 25 da yan bindiga suka kashe a Sakkwato

Tambuwal ya halarci jana’izar mutane 25 da yan bindiga suka kashe a Sakkwato
Source: Facebook

Tunda misalin karfe 5 na yammacin Asabar, 8 ga watan Yuni har zuwa safiyar Lahadi ne yan bindiga suka kaddamar da hare hare a kauyukan Kalhu, Tsage da Geeri dake makwabtaka da garin Gandi, inda suka kashe mutane 25, suka yi awon gaba da shanu fiye da dari, awakai da sauransu.

Karamar hukumar Rabah, garin da aka haifi Sir Ahmadu Bello Sardauna ta sha fama da hare haren yan bindiga a yan kwanakin nan, wanda hakan yayi sanadiyyar asarar rayuka da dama, tare da daidaita daruruwan mutane suka koma zaman sansanin yan gudun hijira.

Tambuwal ya halarci jana’izar mutane 25 da yan bindiga suka kashe a Sakkwato

Tambuwal ya halarci jana’izar mutane 25 da yan bindiga suka kashe a Sakkwato
Source: Facebook

A jawabinsa, Gwamna Tambuwal ya bada tabbacin daukan matakin daya dace don kawo karshen ire iren hare haren nan daya bayyanasu a matsayin hare haren zalunci, don haka yayi kira ga jama’a dasu taimaka ma jami’an tsaro da sahihan bayanai don gudanar da aikinsu.

Shima kwamishinan Yansandan jahar, Ibrahim Kaoje ya bayyana cewa zuwa yanzu sun kama mutane hudu dake da hannu cikin kai harin, daga cikinsu harda wata mata dake kai musu bayanai, wanda ta yi basaja a matsayin mahaukaciya.

Daga kasreh shugaban hukumar kulawa da yan gudun hijira na jahar, Lawal Maidoki yace tuni sun tallafa ma mutanen kauyukan da kayan agaji a sansanonin da suke zaune.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel