Ana zargin Gwamna Sanwo-Olu da batar da miliyoyin kudi a kan motar hawa

Ana zargin Gwamna Sanwo-Olu da batar da miliyoyin kudi a kan motar hawa

Rahotanni na zuwa mana cewa jam’iyyar PDP ta jihar Legas, ta soki sabon gwamna, Babajide Sanwo-Olu da kashe kudi har Naira miliyan 187 domin sayen wata katuwar mota kirar Range Rover.

A wani jawabi da PDP ta fitar ta bakin Sakataren ta na yada labarai na jihar Legas, Taofik Gani, ta bayyana cewa gwamna Jide Sanwo-Olu ya saye katuwar mota ta fiye da miliyan 180 daga hawansa.

Babbar jam’iyyar hamayyar tace gwamnan ya fara mulki ta bai-bai, ganin yadda yayi watsi da manyan ayyukan da abubuwan more rayuwa da Talakawa su ke bukata, ya buge da hawa babbar mota.

Wannan ya sa jam’iyyar adawar ta nemi gwamnan ya fito ya fadawa Duniya ainihin dukiya da kadarorin da ya mallaka. Bayan nan kuma PDP ta na so gwamnan ya salwantar da albashinsa ga marasa karfi.

KU KARANTA: Kabilar Ibo za su iya karbar muki daga hannun Shugaba Buhari

“Idan har Sanwo-Olu ba zai riki halin ta-ka-tsan-tsan da dukiyar al’umma ba, babu wanda zai dauki shirinsa da muhimmanci, ya samu ya ga Likita tun wuri, ya daina kukan cewa ya fara rage nauyi” Inji PDP.

Kakakin jam’iyyar ya kuma bayyana cewa:

“Muddin Sanwo-Olu ya ki bayyanawa Duniya dukiyarsa, za mu yi amfani da dokar FOI domin mu samu bayani a game da duk arzikin da ya mallaka”

Wani Hadimin gwamnan ya karyata duk wadannan zargi inda ya fadawa jam’iyyar adawar cewa ba dole bane mai mulki ya fito ya sanar da Duniya abin da ya mallaka idan zai hau kan mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel