Buhari ya yarda Ibo su karbi mulki bayan 2023 inji Okoloagu

Buhari ya yarda Ibo su karbi mulki bayan 2023 inji Okoloagu

Janar Joseph Okonkwo Okoloagu mai ritaya, wanda Jigo ne na jam’iyyar APC a jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya, ya bayyana cewa Mutanen Ibo za su iya yin mulkin Najeriya nan gaba a 2023.

Joseph Okoloagu wanda yayi takarar Sanatan yankin Arewacin Enugu a APC a zaben da ya gabata, ya bayyana cewa babu wani shugaban kasar da yayi wa mutanen Ibo kokari kamar shugaban kasa Buhari.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana a Ranar Asabar 8 ga Watan Yuni, 2019, Janar Okoloagu ya bayyana duk wannan ne a wata doguwar hira da yayi da ‘yan Jaridar Vanguard a makon da ya gabata.

KU KARANTA: Shugaban APC ba zai bari a gudanar da bincike a kan sa ba

Babban jigon na APC mai mulki yake cewa a lokacin da su ka gana da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa a farkon bara watau 2018, ya bayyana cewa zai yi na’am da batun Ibo su karbi mulki a 2023.

Sai dai kuma Janar Joseph Okoloagu ya kara da cewa akwai gyara a siyasar Ibo har gobe, domin kuwa a cewarsa, ba su da alkibla. Okoloagu yace ya kamata Ibo su samu wata jam’iyya guda su yi karfi.

Jagoran na APC yake cewa babu yadda za ayi yau Ibo su na bayan tafiyar APGA, daga baya su koma su bi jam’iyyar PDP, sannan kuma su yi tunani za su samu mulkin kasar nan a karkashin APC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel