Buhari ya yi maraba da murabus din Alkalin Alkalai Onnoghen

Buhari ya yi maraba da murabus din Alkalin Alkalai Onnoghen

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince, tare da yin marabaa da matakin da korarren Alkalin Alkalan Najeriya, Mai sharia Walter Onnoghen ya dauka na yin murabus daga aiki don kashin kansa.

Legit.ng ta ruwaito shugaban kasa Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa data fito daga bakin kaakakinsa, Malam Garba Shehu a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuni, sa’annan ya umarci mukaddashin Alkalin Alkalai Muhammad Tanko daya nada sabbin Alkalan kotun koli guda 5.

KU KARANTA: EFCC ta janye karar data shigar da Goje bayan ya janye daga takarar shugabancin majalisa

Ya kamata ace Alkali Onnoghen mai shekaru 68 ya cigaba da rike mukaminsa har shekarar 2020, toh amma sakamakon karyar daya gilla ma hukumar da’ar ma’aikata a cikin takardar bayanin arzikinsa tasa aka kunno masa wuta.

Shi dai Alkali Onnoghen da gangan ya boye wasu asusun banki dake makare da dalolin Amurka, wani da fam din kasar Ingila, wani kuma shake da miliyoyin nairori, dukkansu a bankin Standard Chartered Bank.

Wannan bahallatsa ce tayi sanadiyyar shigar da Onnoghen kara gaban kotun da’ar ma’aikata, inda daga karshe shi da kansa yayi murabus a ranar 4 ga watan Afrilu na shekarar 2020, amma sai a ranar Lahadi shugaba Buhari ya amince da matakin.

“Shugaban kasa Buhari ya amince da murabus na kashin kai da mai sharia Walter Onnoghen yayi a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya dsaga ranar 28 ga watan Mayu, 2019, kuma shugaban kasa ya gode masa biya hidimar da yayi ma Najeriya, kuma yana masa fatan alheri.” Inji Garba.

Sai dai jaridar Sahara Reporters ta ruwaito duk da wannan mataki na yin murabus, Onnoghen zai kwashi kimanin naira biliyan 2.5 a matsayin kudin fansho, kudin sallma, kudin kulawa da lafiyarsa har ma dana wasu kananan ma’aikatansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel