Tilas na koma majalisar Buhari - Dalung

Tilas na koma majalisar Buhari - Dalung

Tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung, ya ce babu makawa komawar sa cikin sabuwar majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari a wa'adin sa na biyu ta zamto wajibi da babu wanda ke da ikon dakile tabbatuwar hakan.

Dalung ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar The Punch dangane da takaddamar da ta auku a hukumar wasan kwallon kwando da kuma kungiyar magoya bayan kwallon kafa ta Najeriya yayin shafe wa'adin sa a karagar mulki ta ministan wasanni.

Tsohon ministan ya yi wannan furuci yayin bayar da amsa tare da yiwa manema labarai karin haske dangane da yadda wasu masu ruwa da tsaki ke fafutikar ganin bai samu shiga ba a sabuwar gwamnatin shugaban kasa Buhari.

Yayin bayar da amsar sa cikin yakini na tabbas, Dalung ya ce babu wani haifaffen 'da dake da ikon hana komawar sa ko kuma samun nadin mukami a sabuwar majalisar Buhari matukar Mai Duka ya nufa.

KU KARANTA: Babu kasar da za tayi makwabtaka da kasar Benin ta kwashe lafiya - Dangote

Tsohon ministan wanda ya fito daga jihar Filato ya ce ya yi kwazon gaske wajen tabbatar da nagarta da kuma inganci yayin sauke nauyin da rataya a wuyan sa a ma'aikatar wasanni dake karkashin jagorancin sa.

A yayin da yake jaddada cewar babu wani shamaki tsakanin sa da koma wa kujerar sa a sabuwar gwamnatin Buhari, ya kuma ce ba zai gushe ba wajen kara kaimi na kwatanta kwazon da ya yi a baya domin tabbatar ci gaban kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel