Saraki ya sadaukar da kudinsa ga iyayen Leah Sharibu da wasu mutane 3

Saraki ya sadaukar da kudinsa ga iyayen Leah Sharibu da wasu mutane 3

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya sadaukar da alawus din da zai samu na barin majalisa kacokan ga iyayen wasu mata uku da ayyukan ta’addanci na kungiyar yan ta’addan Boko Haram suka shafa.

Sanata Bukola Saraki ya bayyana haka ne ta bakin Kaakakinsa, Yusuph Olaniyonu ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuni, inda yace baya ga wadannan mata guda uku, Sanatan ya sadaukar da sauran kudin ga iyalan takwarorinsa Sanatoci da suka mutu domin amfanin abinda suka bari.

KU KARANTA: Shahararren dan kwallon Arsenal ya yi aure, shugaban kasa ya halarta

Wadanda zasu amfana da wannan tagomashi sun hada da iyayen Leah Sharibu, dalibar da Boko Haram ta sace daga makarantar yan mata dake garin Dapchi jahar Yobe, sai kuma iyayen Hussaina Ahmed da Hauwa Liman, jami’an bada agaji da Boko Haram suka kashesu.

A watan Feburairun shekarar 2018 ne mayakan Boko Haram suka far ma makarantar Dapchi, suka yi awon gaba da dalibai mata, daga bisani kuma suka dawo dasu, amma suka ki sakin Leah, yayin da su kuma jami’an bada agajin suka shiga hannun kungiyar a watan Oktoban 2018.

Daga cikin kudin, Saraki ya sadaukar da kashi 20 ga iyayen Leah, kashi 20 ga iyayen Hauwa Liman, kashi 20 ga iyayen Hussani, sai kuma sauran kaso 40 da za’ayi amfani dasu wajen kafa gidauniyar da zata taimaka ma iyalan Sanatocin da suka mutu, idan har bukatar hakan ta taso.

Jaridar Premium Times ta ruwaito ana biyan wannan alawus daua kai naira miliyan 7.5 ne ga duk wani Sanatan da ba zai koma majalisar dokokin Najeriya ba, kamar yadda Saraki ya fadi wanwar a kokarinsa na zarcewa akan kujerar Sanata a zaben 2019 daya gabata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel