Buhari ya yi magana a kan kisan mutane 25 a jihhar Sokoto

Buhari ya yi magana a kan kisan mutane 25 a jihhar Sokoto

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya mika sakonsa na ta'aziyya ga gwamnan jihar Sokoto da jama'ar jihar a kan kashe mutane 25 da wasu 'yan bindiga suka yi a karamar Rabah.

"Shugaban kasa ya samu rahoton abinda ya faru a jihar Sokoto dangane da harin da 'yan bindiga suka kai da kuma mutanen da 'yan sanda suka kama dagane da hakan. Shugaban kasa ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamna, Aminu Waziri Tambuwal, da dukkan jama'ar jihar Sokoto.

"Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da dukkan aiyukan ta'addanci a kan jama'ar Najeriya tare da bayar da tabbacin cewar dukkan masu aikata irin wadannan aiyuka masu muni da masu daukan nauyinsu zasu fuskanci fushin doka.

"Ga dukkan wadanda suka samu raunuka, shugaban kasa ya yi musu addu'ar samun sauki cikin gaggawa tare da bayyana cewar gwamnatinsa ba zata taba yin sako-sako ba wajen yaki da 'yan ta'adda, 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan," a cewar jawabin da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ya fitar a ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Abinda yasa muka rasa kujerun gwamna jihohi 5 a zaben 2019 - APC

A kalla mutane 25 'yan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai a wasu kauyuka guda uku dake karkashin karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewar 'yan bindigar sun kai harin ne a kauyukan Kalhu, Tsage da Geeri a ranar Asabar.

A cewar rahotannin, 'yan bindigar sun fara harbe-harbe tun misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar har zuwa safiyar ranar Lahadi. 'Yan bindigar sun yi awon gaba da shanu da tumaki masu yawa bayan kisan mutane.

'Yan bindiga na yawan kai hari a karamar hukumar Rabah a 'yan kwanakin baya bayan nan. Wasu daga cikin mutanen da suka rasa muhallinsu sakamakon harin 'yan bindigar sun koma sansanin 'yan gudun hijira dake Gandi.

Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, ya halarci jana'izar mutanen 25 da aka binne ranar Lahadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel