Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kashe mutane 25 a harin da suka kai Sokoto

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kashe mutane 25 a harin da suka kai Sokoto

A kalla mutane 25 'yan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai a wasu kauyuka guda uku dake karkashin karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewar 'yan bindigar sun kai harin ne a kauyukan Kalhu, Tsage da Geeri a ranar Asabar.

A cewar rahotannin, 'yan bindigar sun fara harbe-harbe tun misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar har zuwa safiyar ranar Lahadi. 'Yan bindigar sun yi awon gaba da shanu da tumaki masu yawa bayan kisan mutane.

'Yan bindiga na yawan kai hari a karamar hukumar Rabah a 'yan kwanakin baya bayan nan. Wasu daga cikin mutanen da suka rasa muhallinsu sakamakon harin 'yan bindigar sun koma sansanin 'yan gudun hijira dake Gandi.

Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, ya halarci jana'izar mutanen 25 da aka binne ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Sabbin ministoci: An leko dalilin da yasa Buhari zai rike wasu ministocinsa 6 a zango na biyu

Da yake magana a gaban shugabannin hukumomin tsaro da masu sarautar gargajiya, gwamna Tambuwal ya mika sakon ta'aziyya ga 'yan uwan wadanda aka kashe.

Da yake magana da manema labarai bayanjana'izar mutanen, Ibrahim Kaoje, kwamishinan 'yan sandan jihar Sokoto, ya ce sun kama mutane hudu da ake zargin na da hannu a cikin harin, cikinsu har da wani mai bawa 'yan bindiga bayanai da ya yi basaja a matsayin mahaukaci.

Kaoje ya kara da cewa rundunar 'yan sanda da hadin gwuiwar ragowar hukumomin tsaro zasu cigaba da aiki tukuru domin magance aiyukan 'yan bindiga da ta'addanci da ragowar miyagun aiyuka a fadin jihar.

Kisan mutanen 25 ya kawo jimillar mutanen da aka kashe a jihar Sokoto zuwa mutum 108 daga shekarar 2018 zuwa yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel