Ana kishin-kishin din Buratai, Sadiq da Olanishakan za su kuma zarcewa

Ana kishin-kishin din Buratai, Sadiq da Olanishakan za su kuma zarcewa

Akwai alamu da ke nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karawa manyan hafsun sojoji Najeriya wa’adi. Shugabannin sojojin na Najeriya za su kara wasu watanni shida a kan kujerunsu.

The Sun ta rahoto cewa shugaban sojin kasa Laftana Janar Tukur Buratai, da shugaban sojojin sama na kasar watau Air Marshall Sadiq Abubakar, da Janar Gabriel Olonisakin duk za su cigaba da zama a ofis.

Shugaban kasar ya dauki wannan mataki ne ganin irin kokarin da jami’an tsaro su kayi wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin babban zaben 2019. Ya kamata dai a ce wa’adin na su ya kare ne a karshen bana.

KU KARANTA: Abin da zai faru idan Buhari yana yi wa shari’a karon-tsaye

Kwanakin baya ne shugaban kasar ta bakin Ministan tsaro ya sanar da cewa hafsun sojin kasar za su cigaba da aiki bayan karewar wa’adin su a 2018. Kanal Tukur Gusau ne ya bada wannan sanarwa lokacin.

Tuni dai manyan sojojin kasar su ka zarce shekarun ritaya a aiki, amma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cigaba da aiki da su a dalilin kwazon da su ka nuna na kawo zaman lafiya a cikin yankunan Najeriya.

Wannan karin wa’adi da shugaban kasar yayi zai fara aiki ne a karshen Watan gobe na Yuli. A dokar Najeriya, shugaban kasa yana da karfin ikon karawa Hafsun sojojin kasar takaitaccen wa’adi na watanni 6.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel