Manyan APC ya kamata su gudanar da bincike a kai na ba kwamiti ba - Shuaibu

Manyan APC ya kamata su gudanar da bincike a kai na ba kwamiti ba - Shuaibu

- Lawan Shaibu ya kalubalanci matakin da Jam’iyyar APC ta dauka na binciken sa

- Shuaibu yace kwamitin da aka kada bai da hurumin da zai gabatar da wani bincike

- Babban Jigon jam’iyyar yana ganin cewa manyan APC ne ya kamata su hukunta sa

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Arewa watau Lawal Shuaibu, ya bayyana cewa ba zai bayyana a gaban kwamitin da aka nada domin ya bincike sa ba. Shuaibu yace kwamitin ba ta da hurumin binciken sa.

Lawal Shuaibu ya tabbatar da cewa ba zai hallara a gaban kwamitin da aka daurawa nauyin binciken sa bane a Ranar Asabar 8 ga Watan Yuni, 2019. Shuaibu ya aikawa wannan kwamiti wasika ne jiya da hannun sa.

Idan ba ku manta ba, a makon da ya gabata, APC ta ta nada kwamiti mai mutum 5 a karkashin Otunba Niyi Adebayo domin binciken zargin da ke kan Sanata Shuaibu na sabawa shugaban jam’iyya Adams Oshiomhole.

KU KARANTA: Sanatocin Najeriya sun bada shaida a kan Bukola Saraki

Kamar yadda APC ta sanar, Sanata Lawan Shuaibu ya yi kokarin tunzura ‘yan majalisar dattawa da wakilai wajen zaben shugabannin majalisar. Shugaban jam’iyyar yace ba zai je ya kare kan sa a gaban wannan kwamiti ba.

A cewar sa:

“Sashe na 21 na dokar APC yace shugabannin zartarwa na jam’iyya ne kurum za su iya binciken wanda ake zargi da laifi don haka ba zan mika kai na a gaban wani haramtaccen kwamiti da aka nada ba…”

“Ina mamakin yadda sha’anin ladabtarwa ya shiga hurumin majalisar NWC na jam’iyya. Duk da ni ba Lauya ba ne, amma na san yadda jam’iyya ta ke aiki, ya kamata ace matakin da aka dauka ya dace da tsarin jam’iyya…”

Sanata Lawan Shuaibu a takardar ta sa ya kara da cewa: “Shawara ta ga Otunba shi ne ya guji yin abin da zai jefa jam’iyya cikin matsala, yayi aiki da abin da doka ta ce.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel