Bankwana da majalisa: Fitattun sanatoci 5 sun bayar da shaida a kan jagorancin Saraki

Bankwana da majalisa: Fitattun sanatoci 5 sun bayar da shaida a kan jagorancin Saraki

A yayin da mambobin majalisun tarayya suka yi zama na karshe biyo bayan karewar wa'adin zangon wakilcinsu a majalisar tarayya karo na 8, wasu sanatocin Najeriya sun yi bankwana da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki.

Wasu fitattun mambobin majlisar dattijai sun bayar da shaida a kan salon jagorancin shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki.

Sanata David Mark - "Shekara ta 20 a zauren majalisar nan, kuma ba tare da wata fargaba ba zan iya cewa kai, Bukola Saraki, ka taka rawar gani wajen daga darajar majalisar dattijai."

Sanata Ali Ndume - "Ina girmama ka sabida tsaya wa kai da fata a kan abinda ka yarda da shi. Bana adawa da kowa saboda biyan bukatar kai na, sai dai don a kan abinda na yi amanna yin sa shine daidai."

Sanata Dino Melaye - "Ina godiya ga ubangiji mai sarrafa kowa da komai. Na sha fada maka cewa kai ne shugaban majalisar dattijai da babu wanda ya isa ya tsige shi. Wadanda aka hada baki da su domin a kai ka kasa yanzu sune ke kiran ka 'maigidansu'. Ranar da na fi kowa farinciki, ita ce ranar da Saraki ya zama shugaban majalisar dattijai."

Sanata Philip Aduda - "Na yaba wa kwazon Dakta Bukola Saraki wajen yin aiki tukuru domin ganin majalisar dattijai ta zartar da dokoki da zasu amfani Najeriya. Ba zan manta da irin matsalolin da majalisar dattijai ta fuskanta ba. In dai maganar majalisa karo na 8 ake yi, tabbas ka yi cancanci a yaba maka."

Sanata Binta Masi Garba – "Babu wani me daraja da ake samunsa cikin sauki, amma tilas wasu lokutan mu ke hakuri da wasu abubuwan. Ina godiya gare ka, Bukola Saraki, shugaba na kuna ubangida na."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel