Babu kasar da za tayi makwabtaka da kasar Benin ta kwashe lafiya - Dangote

Babu kasar da za tayi makwabtaka da kasar Benin ta kwashe lafiya - Dangote

Attajirin da ya yiwa al'ummar nahiyyar Afirka zarra da fintinkau ta dukumar dukiya, Aliko Dangote, ya bayyana takaicin sa dangane da yadda adadin kayayyakin fasakauri ke ci gaba da kutsowa kasar nan daga jamhuriyyar Benin.

Dangote ya bayyana takaicin sa cikin birnin Iko na jihar Legas yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar tsakanin 'yan kasuwa masu zaman kansu da kuma gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Hamshakin dan kasuwar ya ce kayayyaki na fasakauri da kuma harkallar da 'yan sumoga ke ketarowa da su cikin kasar nan ta Najeriya daga kasar Benin na dakile ci gaban masana'antu a kasar nan.

Cikin kalaman sa, Dangote ya ce sumoga da kuma shigowar kayayyaki na fasaukari cikin kasar nan daga jamhuriyyar Benin na babbar nasaba ta kassara duk wani mataki na ci gaba da kasar nan ke fafutikar kai wa.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa 'yan sandan jiha ba su da wuri a Najeriya - Tsav

Ya ce duk kasar da ya kasance ta na makwabtaka da jamhuriyyar Benin ba za ta taba kaiwa zuwa tudun mun tsira ba ta fuskar ci gaban tattalin arziki.

A wani rahoton mai babbar nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito Dangote ya ce Najeriya ta fidda sa ran kai wa tudun mun tsira wajen dawwama cikin koma bayan tattalin arziki matukar wutar lantarki ba ta wadata ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel