Abinda yasa muka rasa kujerun gwamna jihohi 5 a zaben 2019 - APC

Abinda yasa muka rasa kujerun gwamna jihohi 5 a zaben 2019 - APC

- Kakakin jam'iyyar APC na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ya yi waiwaye adon tafiya a kan dalilin da yasa suka rasa wasu jihohi a zaben 2019

- Daga cikin dalilan da Issa-Onilu ya bayyana akwai batun gazawar jam'iyyar na zama mai kwato 'yancin talakan Najeriya

- Kazalika, Kakakin ya caccaki tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif John Odigie-Oyegun, bisa gazawarsa wajen kare jam'iyyar APC daga ta'adin da wasu mambobinta suka yi mata

Jam'iyyar APC mai mulki ta alakanta rasa kujerar gwamna da tayi a wasu jihohi 5 da matsalar raunin da shugabancinta ke da shi.

Kakakin jam'iyyar APC na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan yayin da jaridar New Telegraph ta tattaunawa da shi a kan sabuwar barakar da ta kunno kai cikin jam'iyyar biyo bayan rasa kujerun gwamnonin 5.

APC ta rasa kujerun gwamna a jihohin Oyo, Bauchi, Imo, Adamawa, da Zamfara saboda gaza samun daidaito a tsakanin wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar a jihohin 5. PDP ce ta samu nasara a dukkan jihohin.

Onilu ya bayyana cewar rashin da'a a tsakanin wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar da kuma gazawar jam'iyyar wajen cika alkawuran ceto talaka na daga cikin dalilan faduwar ta zabe a jihohin.

DUBA WANNAN: Hauwa, matar tsohon gwamnan arewa da ya mutu ta auri San Turakin Malumfashi

"Jama'a ba wai sun fi son su zabi PDP ba ne, idan aka duba jihohin da muka fadi daya bayan daya, za a fahimci cewa akwai wasu manyan matsaloli biyu da suka jawowa jam'iyyar APC faduwa zabe.

"Na fardo dai akwai rashin da'a da wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar suka nuna a wadannan jihohi, lamarin da ya haifar da babbar barakar da aka kasa sulhunta wa a tsakanin irin wadannan mambobi.

"Dalili na biyu shine shugabancin jam'iyyar bai yi wani kokari ba daga shekarar 2015 zuwa 2018 wajen ganin ta daidaita sahun tafiyar APC a matsayin jam'iyyar hadin gwuiwa dake da mambobi daga jam'iyyu daban-daban ba," a cewar Isa-Onilu.

Da yake magana a kan tsamar dake tsakanin Oyegun da Oshiomhole, Issa-Onilu ya caccaki tsohon shugaban jam'iyyar tare da bayyana cewar shine silar dukkan matsalolin da jam'iyyar APC ke fuskanta a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel