Dalilin da ya sa 'yan sandan jiha ba su da wuri a Najeriya - Tsav

Dalilin da ya sa 'yan sandan jiha ba su da wuri a Najeriya - Tsav

A yau Lahadi, 9 ga watan Yunin 2019, wani tsohon kwamishinan 'yan sanda, Alhaji Abubakar Tsav, ya ce a halin yanzu Najeriya ba ta taka matakin ci gaba ba wajen samar da 'yan sandan jiha da za su rika gudanar da harkokin tsaro daban daban a jihohin kasar nan.

Duba da mataki na ci gaba, Alhaji Tsav ya ce jihohin kasar nan ba su kai munzalin samun damar kafa hukumomin 'yan sandan su ba daban daban a fagen tabbatar da ingancin harkoki da kuma tsare-tsare na tsaro.

Tsohon kwamishinan 'yan sandan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a babban birnin Makurdi na jihar Benuwai.

Duk da cewar yana goyon bayan wannan kudiri na samar da 'yan sandan jiha a fadin Najeriya, Alhaji Tsav ya ce a halin yanzu hakan ba zai tabbata ba duba da yadda al'amurran wasu 'yan siyasa musamman gwamnoni ke gudana a kasar nan.

Ya ce samar da 'yan sandan jiha a Najeriya na da nasaba da bukatar gudanar da wasu muhimman sauye sauye a kundin tsarin mulkin kasar nan da ba zai tabbata ba cikin sauki ko kuma kankanin lokaci.

KARANTA KUMA: Zargin ku a kan Buhari ba gaskiya bane - MURIC ta yiwa NCEF raddi

Daya daga cikin manyan dalilai da shugaban kasa Muhammmadu Buhari ya zayyana na rashin amincewa da 'yan sandan jiha sun hadar da yadda wasu gwamnonin kasar ke gaza sauke nauyin albashin ma'aikatatun su.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari yayin bayar da madogarar dalilan sa ya ce akwai babbar barazana ta mallakawa 'yan sanda makamai kuma albashin su ya gaza fitowa a lokacin da ya dace.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel