Sabbin ministoci: An leko dalilin da yasa Buhari zai rike wasu ministocinsa 6 a zango na biyu

Sabbin ministoci: An leko dalilin da yasa Buhari zai rike wasu ministocinsa 6 a zango na biyu

Tun kafin karewar zangon wa'adin ministocin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada aka fara hasashen wadanne ministocin ne shugaba Buhari zai cigaba da tafiya da su a zangon mulkinsa na biyu.

Duk da shugaba Buhari ya boye sirrin wadanda zai bawa mukamin minista a sabuwar gwamnatinsa, wasu rahotanni sun bayyana jerin sunayen wasu tsofin ministoci 12 da ake kyautata zaton zasu sake samun mukamin minista a zango na biyu na mulkin Buhari.

Wani rahoto da jaridar 'The Cable' ta buga a ranar Lahadi, ya ba bayyana wasu daga cikin dalilan da ake ganin sune silar dawowar wasu ministoci 6 daga cikin goma sha biyun da aka wallafa. Jaridar ta ce wata majiyarta a fadar shugaban kasa ce ta sanar da ita.

Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ana tsammanin zai koma gwamnatin Buhari duk da saki-na-dafen da ya yiwa jam'iyyar APC a jihar Ribas a takarar kujerar gwamna.

DUBA WANNAN: Majalisar wakilai: Ina takara ne domin gyara kuskuren da APC tayi - Umar Bago

"Buhari zai mayar da Amaechi, hakan a bayyane take. Abun zai yiwa Amaechi yawa idan aka ce Buhari ya ajiye shi. Waye ma wani jigo a jam'iyyar APC daga yankin da ya yiwa Buhari wahala kamar Amaechi?," a cewar majiyar.

Suleiman Adamu, minista albarkatun ruwa, ana tsammanin shi ma zai dawo. Yana daya daga cikin minstocin dake da kusanci da shugaba Buhari. Tun farko ma ya samu minista ne ba don dalilin siyasa ba, sai don alakarsa da shugaba Buhari, wacce ake zargin ta jini ce.

Daga cikin jerin minstocin akwai wadanda aka bayyana cewar zasu koma ne saboda suna da kyakykyawar alaka ta musamman da shugaba Buhari. Wadannan minitoci sune; Hadi Sirika, ministan harkokin jiragen sama, Suleiman Hassan, ministan muhalli, Abdulrahman Dambazau, minsistan harkokin cikin gida, da kuma Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel