Honarabul Bago ya bayyana kuskuren APC a rabon kujerun shugabancin majalisa

Honarabul Bago ya bayyana kuskuren APC a rabon kujerun shugabancin majalisa

Mamba a majalisar wakilai daga jihar Neja, Honarabul Umar Mohammed Bago, ya ce akwai kuskure a cikin shawarar da jam'iyyarsa ta APC ta yanke a kan mika kujerar shugabancin majalisar wakilai zuwa yankin kudu maso yamma.

Bago, mamba mai wakiltar mazabar Chanchaga a karo na uku, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewar ya ki janyewa daga takarar neman kujerar shugabancin majalisar wakilai ne domin gyara kuskuren jam'iyyar APC.

Dan majalisar ya bayyana cewar yankin Kudu maso gabas da yankin Arewa ta tsakiya ne mafi koma baya ta fuskar samun mukamai a rabon kujerun da jam'iyyar APC ta yi. Ya ce APC ta mayar da yankunan biyu saniyar ware.

Ya kara da cewa yana takarar neman kujerar shugabancin majalisar wakilai ne domin zama zabi ga mambobin dake da ra'ayin cewar APC ta mayar da yankinsu saniyar ware a rabon mukaman da jam'iyyar ta yi.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta canja salon tafiyar tuhumar da EFCC ke yi wa Goje

A cewar sa; "ba jayayya muke yi da jam'iyya ba. Muna gwagwarmaya ne domin jawo hankalin jam'iyyar mu a kan kuskuren da ta yi, kuma muna fatan kafin ranar Talata APC zata fito ta ce 'mun yi kuskure', sannan ta gyara kuskuren."

Da aka tambayi Bago a kan ko yana adawa da Gbajabiamila ne saboda zarginsa da tafka badakala a lokacin da yake aikin lauya a kasar Amurka, sai ya kada baki ya ce, "a'a ko kadan ba don haka bane, magana ce kawai ta neman daidaito a rabon mukamai ga kowanne yanki. APC ta ware yankin Arewa ta tsakiya da Kudu maso gabas."

"Yankin da na fito na Arewa ta tsakiya ne ya kamata ya samar da shugaban majalisar wakilai saboda rawar da yankin ya taka a nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zabukan shekarar 2019. Wannan wani abu ne a bayyane da babu wanda zai musanta, alkaluman na nan ga duk mai son tabbatar da hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel