Jam’iyyar APC tana so Omo Agege ya gaji Ike Ekweremadu a Majalisa

Jam’iyyar APC tana so Omo Agege ya gaji Ike Ekweremadu a Majalisa

Mun samu labari a karshen makon nan cewa jam’iyyar APC mai mulki ta reshen Kudu maso Kudancin Najeriya, ta mikawa Sanata Ovie Omo-Agege kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa.

A Ranar Asabar, 8 ga Watan Yuni, 2019, ne jam’iyyar APC na reshen Kudu maso Kudu ta zabi Sanatan jihar Delta, Ovie Omo-Agege, a matsayin wanda zai rike kujerar mataimakin shugaban majalisa.

Shugaban APC na yankin Kudancin kasar, Hilliard Eta da kuma Sakatarensa watau David Okumagba, ne su ka dauki wannan mataki bayan sun yi la’akari da yanayin da siyasar kasar ta ke tafiya.

Tun can jam’iyyar APC mai mulki ta nuna cewa yankin Neja-Delta ne za su fito da mataimakin shugaban majalisar dattawa inda za a kara tsakanin Ovie Omo-Agege da Sanata Francis Alimikhena.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sa-baki a rikicin da APC ta shiga a Jihar Edo

APC ta bayyana cewa Francis Alimikhena mai wakiltar Edo ta Arewa a majalisar da kuma Omo Agege, duk sun cancanci rike wannan matsayi, sai dai an zabi Agege ne saboda a dama da mutanen jihar Delta.

A halin yanzu shugaban jam’iyyar APC ya fito ne daga jihar Edo, don haka shugabannin jam’iyyar na yankin su ka zabi mukamin majalisar ya fito daga jihar Delta wanda ba su da wani babban mukami a APC.

Rahotanni sun ce jagororin jam’iyyar sun kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da Adams Oshiomhole ganin yadda su ke rike kasar da kuma jam’iyyar APC mai mulki, daidai bakin kokarinsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel