Gwamnatin tarayya ta canja salon tuhumar da EFCC ke yi wa Goje

Gwamnatin tarayya ta canja salon tuhumar da EFCC ke yi wa Goje

Tun bayan janyewarsa daga takarar neman kujerar shugaban majalisar dattijai, rahotanni suka fara yada labarin cewar hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta janye tuhumar da take yi wa tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje, a gaban kotu.

Sai dai, Wahab Shittu, lauyan dake kare Goje ya shaidawa manema labarai a ranar Asabar cewar EFCC ba ta janye daga tuhumar da take yiwa Goje ba kamar yadda kafafen yada labarai suka sanar da jama'a.

Da jaridar Punch ta tuntubi Shittu ranar Asabar, ya ce ofishin ministan shari'a ne, bisa dogaro da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya bashi, ya karbi ragamar tuhumar badakalar biliyan N25 da EFCC ke yi wa Goje.

Ya ce hukumar EFCC ba ta da ikon kalubalantar karbar ragamar tuhumar Goje da ofishin ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) ya yi.

"Kundin tsarin mulki ne ya bawa ofishin AGF wannan iko a karkashin sashe na 174 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

DUBA WANNAN: Mambobi 60 na jam'iyyun adawa sun goyi bayan tikitin Gbajabiamila da Wase

"EFCC ba ta da hurumin kalubalantar ikon da ofishin AGF ke da shi.

"Hukumar EFCC ba ta janye kowacce tuhuma ba, ofishin AGF ne ya karbi ragamar tuhumar daga hannun ta," a cewar Shittu.

A ranar Juma'a, 7 ga watan Yuni, ne ministan shari'a, Abubakar Malami, ya karbi ragamar tuhumar Goje daga hannun EFCC.

Hukumar EFCC ta shafe tsawon shekaru takwas tana tuhumar Goje da badakalar biliyan N25.

EFCC ta mika ragamar tuhumar Goje ga Malami yayin wani zaman sauraron tuhumar da ake yi wa Goje a gaban kotun tarayya dake Jos ranar Juma'a. Hakan ta faru ne a gaban alkalin kotun, Jastis Babatunde Quadri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel