Kuri’un Sanatoci na ke nema ba wai sa-hannu a takarda ba – Ali Ndume

Kuri’un Sanatoci na ke nema ba wai sa-hannu a takarda ba – Ali Ndume

Mun samu labari cewa Sanatan kudancin jihar Borno, Mohammed Ali Ndume wanda yake neman kujerar majalisar dattawa yace duk da goyon-bayan da Ahmad Lawan yake samu, ba zai karaya ba.

Sanata Mohammed Ndume yayi watsi da batun goyon bayan da Abokin hamayyarsa ya ke samu, inda har ake cewa Sanatoci fiye da 60 su na tare da Ahmad Lawan a zaben da za ayi a majalisar dattawa.

Babban ‘Dan majalisar jam’iyyar APC mai mulki na kasar yake cewa komai irin yawan Sanatocin da ake rade-radin su na tare da Ahmad Lawan mai wakiltar Yobe ta Arewa, ba zai sa ya janye takararsa ba.

A cewar Ali Ndume, Sanata Lawan na iya samun mubaya’ar ‘yan majalisa, amma kuma ya sha kashi a zaben da za ayi. Sanata Ndume yake cewa babu shakka shi ne yake da ainihin kuri’un ‘yan majalisa.

Sanatan yana mai cewa ba yau ya saba ganin ‘yan majalisa sun yi wa mai neman takara mubaya’a irin wannan ba. Ndume ya tunawa Lawan cewa an yi masa irin wannan mubaya’a a lokacin zaben 2015.

KU KARANTA: An gano wanda 'Yan Majalisa fiye da 180 za su zaba a 2019

Sanata Ndume yace duk da ‘yan majalisa da-dama sun nunawa Ahmad Lawan su na tare da shi a zaben baya da aka yi a 2015, a karshe Bukola Saraki ne yayi nasara a ranar zaben ba shi (Lawan) ba.

“Kun sani sarai cewa zabe dabam da mubaya’a. Idan ba ku manta ba a 2015, an bijiro da irin wannan. Amma a karshe abin da ya faru a zauren majalisa wajen zabe, kuma wani labari ne na dabam.”

“Kamar yadda na fada a baya, da yardar Ubangiji, za mu shiga zabe ne da shirin nasara ko kuma shan kashi. Ni ma nayi nawa lissafin, ba tare da fito da sunayen ‘yan majalisan da ke tare da ni ba.”

A jawabin ‘dan majalisar, ya kara da cewa Abokan aikinsa za su zabi wanda su ka ga ya dace da muradunsu ne idan aka fito ranar zabe, ba wai za su biyewa wata mubaya’a da aka yi a takarda ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel