Edo 2020: Buhari ya sasanta Adams Oshiomhole da Gwamna Obaseki

Edo 2020: Buhari ya sasanta Adams Oshiomhole da Gwamna Obaseki

Mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin rikicin da ake yi a jihar Edo tsakanin manyan jam’iyyar APC, a yayin da ake shirin sake zaben gwamna a shekarar badi mai zuwa.

Wasu jagororin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Edo a karkashin tafiyar Edo Peoples Movement (EPM), sun sha alwashin ganin sun hana gwamna Godwin Obaseki sake samun tikitin jam’iyyar a bana.

Wadannan ‘ya ‘yan jam’iyya da ke ikirarin su na tare da tsohon gwamna Adams Oshiomhole, wanda shi ne shugaban APC na kasa a yanzu, su na zargin Obaseki da kaucewa tafarkin Maigidan na sa.

Shi kuma gwamnan mai neman zarcewa a kan karagar mulki a zaben 2020, ya bayyana cewa wadannan tsiraru a APC da ke adawa da tazarcen sa, ‘yan siyasa ne da ya hana facaka da kudin gwamnati.

KU KARANTA: Ma’aikata sun sha alwashin sa kafar-wando-daya da Gwamna daga hawansa

The Nation ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sa baki a wannan rigima inda ya nemi gwamna mai-ci Obaseki da Adams Oshiomhole su shawo kan duk sabanin da ke tsakaninsu.

Shugaban kasar ya nemi gwamnan na APC da kuma Oshiomhole su zauna ne tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar da kuma manyan jihar Edo. Shugaban kasar ya nemi ayi wannan zama ne a cikin Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnan ya ziyarci shugaba Buhari a Ranar Juma’ar,7 ga Watan Yuni, 2019, a fadar shugaban kasa, inda yayi masa bayani game da shirinsa na sake neman tazarce a zaben 2020.

Majiyar tace a dalilin sa bakin shugaban kasa, Godwin Obaseki da Adams Oshiomhole sun fara magana bayan rikici ya kaure tsakanin gwamnan mai-ci da kuma tsohon gwamnan na jihar Edo a da can.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel