2019: Takarar Dino za ta karawa zaben Gwamna a Kogi armashi

2019: Takarar Dino za ta karawa zaben Gwamna a Kogi armashi

Yayin da ake shiryawa zaben gwamna a jihar Kogi, fitaccen Sanatan PDP na jihar watau Dino Melaye da wasu ‘yan takara fiye da 30 ne su ka nuna sha’awar yin takara da APC a jam’iyyar adawar a bana.

Daga cikin masu harin tikitin PDP akwai tsohon gwamna Idris Wada; da ‘dan uwansa Musa Wada; Dino Melaye; Joseph Erico Ameh; ‘Dan wani tsohon gwamna na jihar, Abubakar Idris; da Emma Omebije

Dino Melaye yana cikin wadanda su ka fara goyon bayan Yahaya Bello bayan rasuwar Marigayi Abubakar Audu a lokacin da ake tsakiyar zaben gwamna a jihar a 2015, kafin rikici ya kaure a tsakani.

Melaye wanda ya sake lashe kujerar Sanata a zaben bana zai nemi ya jarraba sa’ar sa a zaben Nuwamban nan idan ya samu tutar PDP. Masana na ganin Melaye na iya zama barazana ga APC idan ya dace.

KU KARANTA: Abin da ya sa na ba Jonathan mukami a Bayelsa – inji Gwamna Dickson

Jaridar Daily Trust tace sai Sanata Melaye yayi da gaske zai samu takara a PDP ganin yankin da ya fito da kuma cewa ba ya cikin kabilar Igala. Bayan nan, bai kuma dade da dawowa cikin jam’iyyar PDP ba.

Shi ma a na sa bangaren, gwamna mai-ci Yahaya Bello zai nemi ya sake samun tikitin jam’iyyar APC a wannan karo. Idan har yayi nasara, takarar sa da Dino Melaye a karshen bana, za ta zo da ban kaye.

Sauran masu neman takarar kujerar Bello a karkashin jam’iyyar sa ta APC mai mulki sun hada da: Jibrin Usman mai ritaya, Alhaji Yahaya Audu; Sani Lulu; Babatunde Irukera, da kuma Dr Tim Nda Diche

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel