Shugabancin Majalisa: Sanatocin PDP 5 sun goyi bayan Lawan

Shugabancin Majalisa: Sanatocin PDP 5 sun goyi bayan Lawan

Takarar Dakta Ahmad Lawan na neman zama shugaban Majalisar Dattawa karo na 9 ta samu tagomashi yayin da wasu sanatocin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) biyar suka goyi bayansa.

Lawan ya yi matukar jin dadin karamcin da sanatocin na jam'iyyar adawar suka nuna masa a yayin da ya ke gabatar da shiri na musamman na majalsar da ya yi wa lakabi da "Majalisar Tarayyar da za ta yi wa dukkan 'yan Najeriya aiki."

Sanatocin na PDP sun hada da Abba Moro (Benue ta Kudu), Mathew Urgohide (Edo ta Kudu), Cliford Ordia (Edo ta Tsakiya), Gershom Bassey (Cross River ta Kudu) da Lawali Anka (Zamfara ta Yamma).

DUBA WANNAN: Daga karshe: Sarki Sanusi ya amsa tuhumar da Ganduje ke masa

Lawan ya gabatar da jawabinsa inda ya lissafo wasu abubuwa guda bakwai da zai aiwatar idan ya yi nasarar zama shugaban na majalisar.

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoto inda Ahmad Lawan ya ce akwai sanatocin jam'iyyar PDP masu yawa da ke goyon bayan takararsa na shugabancin majalisar dattawa.

A hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Abuja, Lawan ya yi alkawarin cewa ba zai bawa abokan aikinsa kunya ba muddin suka zabe shi.

Lawan ya samu goyon baya daga shugabanin jam'iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) har da da shugaba Muhammadu Buhari sai dai hakan bai hana wasu daga cikin abokan aikinsa daga bangaren Arewa maso Gabas neman takarar kujerar ba.

Amma daga bisani Sanata Goje ya janye takarsa inda shima ya ce zai marawa Lawan baya wadda haka ne nuna cewa bisa ga dukkan alamu Lawan ne zai yi nasarar zama shugaban na majalisar ta 9.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel