Gwamna Masari ya yi sabbin nade-nade 3 masu muhimmanci

Gwamna Masari ya yi sabbin nade-nade 3 masu muhimmanci

Gwamna Masari na Jihar Katsina ya amince da sake nada Alhaji Mustapha Inuwa a matsayin Sakataren Gwamnatin jiha (SSG).

Alhaji Falulu Bawale, Direktan Harkokin Mulki na gidan gwamnati ne ya bayar da sanawar cikin wata jawabi da ya fitar a ranar Asabar 8 ga watan Yunin 2019.

A cewar Bawale, gwamnan ya kuma sake nada Mista Muntari Lawan a matsayin Famanen Sakatare kuma mai bayar da shawara na musamman a gidan gwamnati da Mista Abdu Labaran a matsayin babban mai bayar da shawara na musamman (SSA) kan kafafen yada labarai.

DUBA WANNAN: Har yanzu Ganduje da Sanusi ba su yi sulhu ba - Hadimin Gwamna

Ya ce gwamnan ya sake yi musu nadin ne duba da irin jajircewa da gwazo da suka nuna wurin yi wa jihar hidima yayin mulkin gwamnan zango na farko.

Nadin na su zai fara aiki nan ta ke kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel