Borno: Gwamnna Zulum ya yi nasara kan tsohon minista da sauransu a kotu

Borno: Gwamnna Zulum ya yi nasara kan tsohon minista da sauransu a kotu

Karo na hudu a jere, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umar Zulum na kayar da wata kungiyar masu daukaka kara da suka hada da tsohon karamin ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje, Mustapha Baba Shehu; wani dan takarar gwamna a 2003, 2007, 2011, 2015 da kuma 2019, Alhaji Kashim Imam, wani tsohon Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Mohammed Umara Kumalia, wani daraktan kudi a ma’aikatar noma ta tarayya, Idrissa Mamman Gatumba, da wasu biyu duk yan APC a kotun daukaka kara.

Sun dai shigar da kara ne da ke kalubalantar zaben fidda gwani na gwamna a jihar Borno wanda aka gudanar a watan Oktoban 2018, inda Zulum ya yi nasara.

Masu karar sun yi takarar zaben fidda gwani na gwamna a karkashin jam’iyyar APC amma suka sha kaye a hannun Zulum. Bayan zaben, sai suka tunkari kotun tarayya da ke zama a Maiduguri inda suka bukaci kotu ta soke nasarar Zulum.

Sun sha kaye a kotun tarayyar, sannan kuma suka sha kaye a kotun daukaka kara da ke Jos, don haka suka kara komawa kotun tarayya a Maiduguri kafin su sake daukaka kara, wanda a yanzu suka sake shan kaye a ranar Juma’a.

KU KARANTA KUMA: Kaakakin majalisar wakilai: Yan majalisa 183 sun mara wa Gbajabiamila baya

A hukuncin kotun daukaka kara wandan Justis U. Onyemenam, da taimakon Justis MN Oniyangi da BM Ugo, sun yi watsi da karar da aka shigar kan Zulum, APC da INEC, cewa karar bai da inganci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel