Kaakakin majalisar wakilai: Yan majalisa 183 sun mara wa Gbajabiamila baya

Kaakakin majalisar wakilai: Yan majalisa 183 sun mara wa Gbajabiamila baya

Jimlan yan majalisa 183 cikin 360 ne suka sanya hannu domin mara wa takarar Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila (APC, Lagos), domin darewa kujerar kakakin majalisar wakilai na tara gabannin rantsar dasu a ranar Talata, 11 ga watan Yuni.

Shugaban kungiyar kamfen din Gbajabiamila/Wase, Abdulmumin Jibrin (APC, Kano) wanda ya bayyana hakan a Abuja a ranar Asabar, 8 ga watan Yuni ya bayar da tabbacin cewa suna sanya rai ga nasarar dan majalisar na jihar Lagas.

A cewar Jibrin, goyon bayan ya samu ne daga sabbin zababbun yan majalisa a fadin sassa shida na kasar.

“A yanzu haka da nake maku Magana, muna da abunda ake bukata domin lashe kujerar a ranar Talata, 11 ga wata Yuni. Ina nufin muna da adadin mutanen da ake bukata. Sama da zababbun mambobin majalisa 183 sun sanya hannu don goyon bayan Gbajabiamila da Wase a matsayin kakakin majalisar wakilai da mataimakinsa,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Buhari da Tinubu sun dakatar da kulla-kullar tsige Oshiomhole daga kujerarsa

Wadanda ke takarar kujerar kakakin majalisar wakilai da Gbajabiamila sun hada da Umaru Bago (APC, Niger); Nkeiruka Onyejeocha (APC, Abia); da kuma John Dyegh ( APC, Benue).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel