Gbajabiamila zai ba PDP mukamai 60 a sabuwar majalisar wakilai

Gbajabiamila zai ba PDP mukamai 60 a sabuwar majalisar wakilai

-Femi Gbajabiamila yayi alkawarin mukamai ga mambobi 60 'yan jam'iyar PDP idan har ya yi nasarar kasancewa kaakakin majalisar ta wakilai.

-Daraktan kamfen na Femi/Wase, Abdulmumin Jibrin ne ya bada wannan labari ga manema labarai ranar Asabar a Babban birnin tarayya.

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila ya yi alkawarin mukamai 60 ga zababbun yan majalisar PDP wanda zai kunshi shugabancin kwamitocin majalisar idan har aka zabe shi kaakakin majalisa ta 9.

Jagoran tawagar kamfen na Femi/Wase, Abdulmumin Jibrin ne ya bayyana wannan zance a wata zantawa da ya yi da manema labarai ranar Asabar a Abuja.

KU KARANTA:Zaben 2019: Ku bamu shahadarmu, zababbun yan majalisa 5 na Bauchi sun fada wa INEC

Jibrin ya ce: “ Yan majalisa 60 na jam’iyar PDP sun aminta da wannan tayi da aka yi masu, kuma tuni suka fara shirin hada karfi da karfe da takwarorinsu na APC domin tabbatar da cewa Gbajabiamila ya kawo wannan kujera.”

Sai dai kuma dan majalisar wanda ya fito daga Kano ya ce: “ Yayin kulla wannan yarjejeniya da mambobi 60 na PDP wadanda suka riga suka amince, tawagarmu na cigaba da tattaunawa da dayan bangaren na jam’iyar PDP.”

Jibrin ya ce: “ In dan ta mambobin APC ne bamu da matsala daga bangarensu, kuri’arsu gaba dayanta tamu ce. Kafin a gabatar da Femi a matsayin dan takarar kaakakin majalisa, shugaban kasa da gwamnoni sun riga sun fadi cewa wannan shi ne kaakakin da ya dace da majalisarmu.”

Jagoran kamfen na Femi/Wase ya cigaba da cewa: “ A halin yanzu muna da goyon bayan mafi rinjaye daga jam’iyarmu da kuma sauran jam’iyun dake da wakilci a majalisa. Mun riga da mun samu goyon bayan mutum 60 daga PDP daya bangaren ma muna cigaba da tattaunawa dasu domin cinma matsaya guda."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel