Daga karshe: Sarki Sanusi ya amsa tuhumar da Ganduje ke masa

Daga karshe: Sarki Sanusi ya amsa tuhumar da Ganduje ke masa

Sarkin Kano, Mallam Sanusi Muhammad Sanusi II ya amsa tuhumar da gwamnatin Jihar Kano ta ke masa kan zargin bannatar da naira biliyan 3.4.

A cikin amsar da ya bayar cikin wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren masarautan, Alhaji Abba Yusuf, Sarkin Kanon ya ce naira biliyan 1.8 kacal ya tarar a asusun masarautan.

Sarkin ya kuma ce ba za a iya tuhumarsa da almubazarancin kudi ba saboda ba shine jami'in da ke kula da kudaden masarautar ba.

Wasikar da mai kwanan wata ranar 7 ga wata Yunin 2019, ta ce: "Ina son sanar da kai cewa a lokacin da mai martaba ya zama sarkin Kano, adadin kudin da ke asusun masarautar shine N1,893,378,927.38.

DUBA WANNAN: Kalli bidiyon wasu fastoci 2 da suka musulunta cikin watan Ramadan

"Yana da kyau a fahimta cewa mai martaba ba shi ne jami'in kula da kudade na masarautar Kano ba, shi sakataren masarautar ne."

Sarkin ya mika godiyarsa ga gwamnatin Kano saboda ba shi damar kare kansa daga zargin da a kayi masa cikin rahoton da hukumar sauraron korafe-korafen al'umma da yaki da rashawa na jihar ta yi masa.

Idan ba a manta ba, Hukumar Yaki da Rashawar ta Kano ta zargi sarkin da wasu mukarranbansa hudu da barnatar da naira biliyan 3.4.

Sarki Sanusi ya amsa tuhumar da gwamnatin jihar ke masa duk da cewa ana tattaunawar sulhu tsakaninsa da Gwamna Abdullahi Ganduje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel