Gwamnan Bauchi ya yi kyautar kudi ga marasa lafiyan dake asibiti

Gwamnan Bauchi ya yi kyautar kudi ga marasa lafiyan dake asibiti

- Bala Muhammad ya bada kyautar kudi ga marasa lafiyan dake ke kwance a asbitin kwararru ta jihar Bauchi

- Dakta Sani Adamu na sashen GOPD dake asibitin ne ya labarta wannan zancen ga 'yan jarida inda yake cewa tare da shi suka kewaya asbitin da mai girma gwamnan

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi a jiya Juma’a ya bada kyautar N5,000 ga dukkanin marasa lafiyan dake kwance a asibitin kwararrun jihar.

Ya yi wannan kyautar ne a lokacin ziyarar barka da sallah wacce ya kai asibitin. Shugaban sashen GOPD na asibitin, Dakta Sani Adamu ne ya bayyana wannan labari ga ‘yan jarida.

KU KARANTA: Zaben 2019: Ku bamu shahadarmu, zababbun yan majalisa 5 na Bauchi sun fada wa INEC

Shugaban ya fadi cewa: “ Na zagaya da gwamna zuwa bangarori daban daban na asibitin, inda ake kwantar da yara kanana, mata masu juna biyu da kuma bangaren tiyata inda ya bada kyautar kudi zuwa ga marasa lafiyan.”

Haka zalika, “Gwamnan ya biya kudin sayen magunguna da kuma kayayyakin aikin tiyata ga wadanda basu da halin biya. Ma’aikatan asibitin dake aiki a wannan lokacin sun samu kyautar wadannan kudade.”

Adamu ya roki gwamnati kan ta karo ma’aikata a asibitin domin cigaba da ba wa lafiya kula ta musamman. Har wa yau, ya sake kira ga gwamnati cewa a samar da wadatattun kudade ga asibitin domin kula da lantarki saboda gudanar da wasu manya-manyan ayyuka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel