Sulhun da aka yi tsakanin Ganduje da Sanusi ya sanya farin ciki a zukatan al’umman Kano

Sulhun da aka yi tsakanin Ganduje da Sanusi ya sanya farin ciki a zukatan al’umman Kano

Al’umman jihar Kano sun yaba da sulhun da aka yi tsakanin gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Wata kwamiti karkashin jagorancin Aliko Dangote da Gwamna Kayode Fayemi ne suka jagoranci yin sulhu a tsakanin nasu a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuni a babbar birnin tarayya, Abuja.

Wasu mazauna jihar, da suka zanta da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), a ranar Asabar a Kano sun nuna ammanna da godiya da sulhun da aka yi.

A cewar wasun su, hakan zai kawo zaman lafiya a zjihar dama kasa baki daya.

Abba Ahmed, wani jami’in gwamnati mai ritaya a jihar, yace sulhun zai kawo sauki da kwanciyar hankali a zukatan mazauna jihar.

“Hankalina a tashe yake tunda lamarin ya fara, musamman kasancewar ina da zama a kusa da masarautar inda hankalin mutane yaki karkata kan lamarin.”

Yayi bayanin cewa lamari na daya daga cikin munanan abubuwa da ya faru da Kano. Ya yaba ma kwamitin Dangote akan matakinta.

Nura Muhammad, wani ma’aikacin gwamnati, ya bayyana cewa sulhu ya zo a kan lokaci, domin zai kare dukkanin arewacin Najeriya daga matsaloli da dama.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokokin Kaduna ta yi na’am da kudirin yi wa ayyukan addini iyaka a jihar

Muhammad Ahmad, wani dan kasuwa, yace sulhun ya ceci Kano daga shan kunya saboda abubuwan da ka iya tasowa idan aka ci gaba da rigimar.

Ya bukaci mazauna jihar da su ci gaba da addu’an zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya sannan a guji abubuwan da ka iya haddasa rikici musamman a lamarin siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel