Buhari da Tinubu sun dakatar da kulla-kullar tsige Oshiomhole daga kujerarsa

Buhari da Tinubu sun dakatar da kulla-kullar tsige Oshiomhole daga kujerarsa

- Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta bayyana cewa har yanzu Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, na da goyon bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jigon jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu

- Majiyar ta lura cewa har yanzu Buhari a Tinub sun yarda da karfin Oshiomhole na jagorantar jam’iyyar duk da kayen zabe da APC ta sha a wasu jihohi

Rahotanni da ke billowa sun nuna cewa shugaba jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole, na iya tsere ma makircin da ake na tsige shi daga kujerarsa ta karfin tuwo, bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban jigon jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun sanya baki.

Wata majiya da ke sane a abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar ta fada ma jaridar Vanguard cewa Buhari da Tinubu sun yi imani da karfin Oshiomhole na jagorantar jam’iyyar duk da kayen zabe da APC ta sha a was jihohi.

Majiyar tace wasu daga cikin samu ruwa da tsaki na jam’iyyar da suka cire tsammani a karfin Oshiomhole wajen jagorantar jam’iyyar sun dawo a yanzu suna goyon bayansa saboda goyon bayan da ya samu daga Shugaban kasar da babban jigon jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Bayan shekaru da yawa: Anyi wa fursuna mafi tsufa a Najeriya afuwa

“Tunda dai mutane biyun da suka kawo shi kan mulki na goyon bayansa har yanzu, babu inda Oshiomhole zai je, ni na fada maku haka. Kun ga cewa Shuaibu shi kadai yake kidinsa da rawarsa hakan ne yasa basu gayyace shi zuwa taron kwamitin masu ruwa da tsaki ba a jiya,” inji majiyar.

“Da Oyegun ya fara yakar Asiwaju wanda ya kawo shi mulki sannan da matsin lamba ya kunno kai, bai kai labari ba saboda baida babban bangon jingina a bayansa, amma ba wannan bane bayani a yanzu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel