Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un: Fasinjoji 18 sun kone kurmus a hadarin mota

Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un: Fasinjoji 18 sun kone kurmus a hadarin mota

Fasinjoji 18 sun rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su a ranar Asabar kan hanyar Akure zuwa Owo.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne a lokacin da wata motar bus ta yi karo da wata babban mota wadda hakan ya sa wasu motocci biyu suka kama da wuta.

Mista Femi Joseph, Kakakin Rundunar 'Yan sandan jihar Ondo ya ce gawarwakin wadanda suka rasu yana dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Kwararru na Akure.

DUBA WANNAN: Ka bawa masu bincike hadin kai - Yakasai ya fadawa Sarki Sanusi

Kakakin Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC) reshen Jihar Ondo, Olusegun Ogungbemide shima ya tabbatar da afkuwar hatsarin.

Ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne yayin da direbobin ke kokarin kaucewa rami a titi alhalin suna gudu fiye da ka'ida.

Ya ki kira da direbobi su kiyaye ka'idojin tuki domin kaucewa afkuwar haddura a titi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel