Bayan shekaru da yawa: Anyi wa fursuna mafi tsufa a Najeriya afuwa

Bayan shekaru da yawa: Anyi wa fursuna mafi tsufa a Najeriya afuwa

Rahotanni sun kawo cewa an yiwa wani fursuna mafi tsufan shekaru a gidan kurkukun Najeriya afuwa bayan ya shafe shekaru a tsare.

Dattijon wanda aka ambata da suna Celestine Egbunuche ya shafe shekara 18 a gidan yari bayan yanke masa hukuncin yunkurin yin kisan kai.

Egbunuche ya hadu da 'yarsa bayan fitowarsa daga gidan yarin Jihar Enugu.

Wata kungiya mai zaman kanta da ke yaki da rashawa ce ta yi gwagwarmayar ganin an sake shi.

'Yarsa mai suna Chisom Celestine ta bayyana cewa tana cike da farin ciki. "Muna godiya da wannan rana."

Dattijon ya yi fama da rashin lafiya sosai a gidan yari, inda yake fama da cutar ciwon siga da matsalar ido.

Yanzu haka yana asibiti ana duba lafiyar shi, yayin da babu tabbas kan ko mai zai iya faruwa da shi nan gaba.

KU KARANTA KUMA: Kalli uwargidar gwamnan jihar Gombe da ke sanya dogon hijabi har kasa

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa undunar yan sandan jihar Kano sun haramta duk wani gangami ko taron jama’a a jihar har sai baba-ya-gani.

Umurnin na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna, wanda aka bai wa manema labarai a Kano a ranar Asabar, 8 ga watan Yuni.

Haka zalika yace rundunar ya janye izinin da ta baiwa jama’a, kungiyoyi, jam’iyyun siyasa, kungiyoyi masu zaman kansu da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel