Kaakakin majalisa: An nemi Dogara ya koma karo na 2

Kaakakin majalisa: An nemi Dogara ya koma karo na 2

- Wata kungiya mai goyon bayan jam'iyar PDP jihar Bauchi ta nemi kaakakin majalisa, Yakubu Dogara da ya sake tsayawa takarar kujerarsa a karo na biyu.

- A cewar kungiyar kaakakin majalisar ya gudanar da ayyuka da dama cikin shekaru hudun da ya yi a kan kujerar tasa ta kaakakin majalisar wakilai.

Gamayyar kungiyar magoya bayan jam’iyar PDP a jihar Bauchi ta nemi kaakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya sake tsayawa takarar kujerarsa a karo na biyu.

Kungiyar mai suna Freedom Amalgamated Youths Organisations (FAYO) a wani taron ganganmi da ta yi ranar Asabar a Bauchi ta ce Dogara yayi abin a yaba masa cikin shekaru hudu da ya yi a matsayinsa na kaakakin majalisar wakilai.

Suleman Shehu wanda shi ne shugaban kungiyar ya bayyana cewa, “ Wannan kungiyar ta mu ta fahimci muhimmancin sake takarar Dogara bisa ga la’akari da kyawawan ayyukan da yake yi a matakin kasa da kuma gundumarsa baki daya.”

A cewar kungiyar, kaakakin ya kawo cigaba ta fanni daban daban a gundumarsa da ma wasu wuraren na daban.

KU KARANTA: Shugabancin majalisar dattawa: Sanatoci 61 sun lamuncewa Lawan – Kungiyar kamfen

Har ila yau, Dogara ya taka muhimmiyar rawa a bangaren cigaban jihar Bauchi da ma Arewacin Najeriya, daya daga cikin abinda ya aikata shi ne sanya hannu cikin kaddamar da hukumar cigaban Arewa maso gabas wato NEDC.

Shehu ya ce: “Kaddamar da wannan hukuma zai taimaka kwarai da gaske domin magance matsalolin dake addabar yankin Arewa maso gabas.”

A karshe shugaban ya yi kira ga jama’ar Bauchi musamman magoya bayan jam’iyar PDP da gwamna Bala Muhammad a kan su sa baki tare da marawa kaakakin baya don ya sake tsayawa takarar kujerarsa a karo na biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel