Yan sanda sun haramta gangami da taron jama’a a Kano

Yan sanda sun haramta gangami da taron jama’a a Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano sun haramta duk wani gangami ko taron jama’a a jihar har sai baba-ya-gani.

Umurnin na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna, wanda aka bai wa manema labarai a Kano a ranar Asabar, 8 ga watan Yuni.

Haka zalika yace rundunar ya janye izinin da ta baiwa jama’a, kungiyoyi, jam’iyyun siyasa, kungiyoyi masu zaman kansu da sauransu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa umurnin baya rasa nasaba da tashin hankalin da aka samu biyo bayan takardar neman ba’asi da aka aike wa sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, kan zargin almubazaranci da naira biliyan 3.4 na masarautar karkashin jagorancin Sanusin.

Yayi bayanin cewa akwai bukatar daukar wannan mataki domin guje ma saba doka da oda ta fuskacin tsaro a jihar.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda da SSS sun mamaye wajen AIT yayinda aka sake bude tashar

Yayi gargadin cewa idan aka kama wani mutum ko kungiya da suka tara jama’a ba bisa ka’ida ba toh za su fuskacin hukunci.

Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bin haka har sai illa masha Allah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel