Yan sanda da SSS sun mamaye wajen AIT yayinda aka sake bude tashar

Yan sanda da SSS sun mamaye wajen AIT yayinda aka sake bude tashar

Hukumomin tsaron Najeriya sun yi wa harabar gidan talbijin din African Independent Television (AIT) kawanya bayan a sake bude tashar talbijin din a raar Juma’a, 7 ga watan Yuni, wani jami’i ya bayyana.

Gidan talbijin din mai zaman kanta ta bude a ranar Juma’a bayan rufe ta da hukumar kula da tashohin labarai a kasa (NBC) tayi na tsawon sa’o’i 24.

Wata kotun tarayya da ke Abuja ce ta soke dakatarwar da gwamnati tayi wa tashar labaran sannan ta bukaci ta koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.

Amma jim kadan bayan ta fara auki, sai hukumomin tsaro suka yi kawanya a harabar tashar, a cewar manajan daraktan tashar, Tony Akiotu.

KU KARATA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi sun yi sulhu

Da misalin karfe 12:30 na tsakar daren jiya Juma’a, jami’an tsaro da suka hada da yan sanda da SSS na nan kewaye da tashar na kamfanin DAAR Communications Plc, cewar Mista Akiotu a sakon da aikewa jaridar Premium Times da safiyar yau Asabar.

Sun zo “dauke da manyan makamai sannan suna ta zagaye harabar,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel