Za mu bi umurnin kotu akan Rochas Okorocha - INEC

Za mu bi umurnin kotu akan Rochas Okorocha - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tace za ta bi huku ci babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin jagorancin Justis Okong Abang, wanda yayi umurnin ba tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha takardar shaidar cin zabe a matsayin zababben sanata a yankin Imo ta yamma.

Kwamishinan hukumar zaben na kasa kuma Shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, wanda ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a jiya Juma’a, 7 ga watan Yni, yace hukumar na sane da umurnin babbar kotu n jihar Imo karkashi jagorancin Justis Njemanze day ace kada taba kowani dan takara takardar shaidar cin zabe a zaben yankin Imo ta yamma.

“A yanzu haka hukumar a sake duba ga zaben 2019 a matakin jiha sannan dukkain kwamishinoninta na kasa ka jagorantar aiki lura da abubuwan da suka shafi nazarin.

“Baya ga hukuncin kotu, hukumar za ta gana ba da jimawa ba domin yin abunda ya kamata. A matsayinta na hukuma mai bin doka, za taici gaba da bin umurni dukkanin kotun shari’a,” inji Okoye.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi sun yi sulhu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata kotun tarayya da ke Abuja ta soke hukuncin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na kin ba tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha takardar shaidar cin zabensa a matsayin zababben sanata.

Kotun ta bayyana cewa hukuncin hana Mista Okorocha takardar cin zabensa ya saba ma doka don haka hukunci ne da baya bisa ka’ida.

A cewar kotun karkashin jagorancin Justis Okong Abang, baturen zaben hukumar INEC ne kadai ke da ikon kaddamar da mutum a matsayin mai nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel