Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da dokar sa ido a kan harkokin addini

Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da dokar sa ido a kan harkokin addini

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, a ranar Juma'a ta amince da dokar sa ido kan harkokin addini na shekarar 1984.

Majalisar ta amince da kudirin dokan ne mintuna kadan kafin kakakin majalisar, Aminu Abdullahi Shagali ya rushe ta biyar.

A yayin zaman majalisar, kakakin majalisar, Aminu Abdullahi Shagali ya ce an kafa hukumar ta sa ido kan harkokin addinin da ciyaman din ta bisa umurnin sakataren gwamnatin jihar.

Ya kuma ce gwamnan jihar zai nada mutane biyu da za su wakilci musulmi da kirista da ma wasu nade-naden.

DUBA WANNAN: Daga karshe: Buhari ya saka baki cikin rikicin Ganduje da Sanusi

Ya ce bayan gwamna ya saka hannu kan dokar, za a kafa kwamitin tattaunawa tsakanin addinai a dukkan kananan hukumomi 23 da ke jihar ta Kaduna.

Dokar ta ce duk wani da aka samu ya saka wa'azi da na'urar amsa kuwwa tsakanin karfe 11 na dare zuwa 4 na asuba indan ba a masallaci ko coci bane ya aikata laifi da za a iya cin sa tarar da ba ta gaza N200,000 ko daurin gidan yari na a kalla shekaru biyu ko dukka biyun.

Bugu da kari, dokar ta kuma ce duk wanda aka samu yana zagi ko tunzura al'umma yayin wa'azinsa ko karya zai fuskanci hukuncin daurin shekara biyar ko tara N100,000.

Majalisar ta amince da dokar ne shekaru uku bayan gabatar duba da cewa kungiyoyin addinai da dama a jihar ba su gamsu da ita da farko ba.

Majalisar za ta aike wa gwamna Nasir El-Rufai domin ya rattaba hannu a kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel