Yan sanda sun kama masu laifi 90 a jihar Kano

Yan sanda sun kama masu laifi 90 a jihar Kano

Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Kano tace ta kama masu laifi 90 a birnin Kano a cikin makon da ya gabata. Kwamishinan yan sanda, Mista Ahmed Iliyasu, ya bayyana hakan ne yayin da yake bayyana masu laifin ga manema labara a hedikwatan yan sanda dake Bompai a Kano a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa masu an kama masu laifin ne a lokacin da rundunan ta addabi mafakar masu laifin a yankunan jihar a ranar Talata da Laraba.

Kwamishinan ya fada cewa an kama masu laifin a yankin Gano, karamar hukumar Dawakin Kudu; Bachirawa quarters, karamar hukumar Ungoggo da hanyar Fadar Sarki a birnin Kano.

Ya bayyana cewa sauran yankuna inda aka kama masu laifi sun hada da Dala, Panshekara, Kwana Hudu da Dakata quarters, duk a cikin birnin Kano.

Ya bayyana cewa daga cikin kayayyakin da aka kwace sun hada da wukake 64, almakashi, gatari, abun yankan karafina, layoyi, mahadin tabar wiwi da kayan shaye shaye.

Bugu da kari shugaban yan sandan yace har ila yau an kama mutane biyu da manyan buhunan mahadin tabar wiwi har na naira miliyan 5 a Dala quarters a Kano.

Ya bayyana cewa yan sandan rashen Dala sun kama masu laifin biyu a ranar Laraba, misalin karfe 6 na yamma bayan sun samu bayanai mai amfani.

KU KARANTA KUMA: Barayi sun harbi wani mutum sannan suka yi masa fashin N1.5m a Bauchi

A wani lamari mai kama da haka, ya fada cewa yayin da rundunan ke faturol a unguwan fadar sarki a ranar sallah, rundunan ta kama mutane 25 wadanda ake zargi a kisan mutun daya da kuma raunata mutane da dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel