Mutane 3 sun halaka a sanadiyyar tashin bom a jahar Imo

Mutane 3 sun halaka a sanadiyyar tashin bom a jahar Imo

Rundunar Yansandan jahar Imo ta sanar da cewa wani bom ya tashi a jahar, kuma yayi sanadiyyar mutuwar mutane uku, kamar yadda kaakakin rundunar, Orlando Ikeokwo ya bayyana a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin yana cewa lamarin ya faru ne a kauyen Eziorsu dake cikin karamar hukumar Oguta ta jahar Imo, sa’annan ya bayyana sunayen wadanda bom ya tasa kamar haka; Elvis Ukado; Kasiemobi Uzoma da Justice Adie.

KU KARANTA: EFCC ta janye karar data shigar da Goje bayan ya janye daga takarar shugabancin majalisa

“Bom din na jibge ne a wani bolan da ake ajiye karafa marasa amfani, kuma ya tashi ne a lokacin da guda daga cikin mutanen da suka mutu yake dukan bom din da nufin lotsashi a zatonsa karfe ne.” Inji shi.

Haka zalika kaakakin ya bayyana cewa tuni kwamishinan Yansandan jahar Imo, Rabiu Ladodo ya kai ziyara zuwa inda lamarin ya faru, sa’annan yayi kira ga jama’a dasu sanar da hukumar duk wani karfe da suke zaton bom ne.

“Kwamishinan Yansanda na kira ga jama’a dasu isar da sakon duk wani karfen da basu gane yanayinsa ba domin watakila tsohon bom ne, ta haka ne zamu iya duba shi domin tabbatarwa, mu daukeshi har ma mu lalatashi ba tare da yayi ma jama’a illa ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel