Lamarin Almajiranci zai dame mu sosai a nan gaba – Tambuwal

Lamarin Almajiranci zai dame mu sosai a nan gaba – Tambuwal

- Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya nuna tsoro kan yadda almajirai da ke barace-barace ke daukar wasu munanan dabi’u masu hatsari

- Tambuwal ya bayyana cewa hakan zai dame su sosai a nan gaba kadan

- Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga manema labarai bayan wata ganawa da manyan mutane yan asalin Sokoto a fadar sarkin Musulmi

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya nuna tsoro kan yadda almajirai da ke barace-barace ke daukar wasu munanan dabi’u masu hatsari “wanda zai dame mu sosai a nan gaba kadan.”

Gwamnan yace: “Ya kamata ace yaranmu na zuwa makaranta ba wai fakewa a karkashin tsarin Almajiranci ba wajen fara barace-barace.”

Tambuwal ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga manema labarai bayan wata ganawa da manyan mutane yan asalin Sokoto a fadar sarkin Musulmi.

“Gwamnatin jihar yayinda take nuna kulawarta tana kan tattauana lamarin tsarin barace-baracen almajirai sannan nan ba da jimawa ba za ta kira wadanda abun ya shafa domin neman mafita mai dorewa,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da Hakimai 2 saboda rashin biyayya ga masarautar Rano

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa rundunar 'yan sandan jihar Osun ta kama wani malamin addinin Musulunci mai suna Alfa Majid Olore, bayan an gano wani gida da yake satar mutane yana boye a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Jaridar Independent ta bada rahoton an kama Alfa tare da matarsa da 'ya'yansa da kuma sama da Almajiransa 55, wadanda ke zama a Ita Baale a cikin garin Ibadan. Haka kuma kimanin mutane 20 rundunar 'yan sanda suka kama a yankin Ita Baale.

A cewar wani wanda lamarin ya faru akan idonsa, mutanen da ake zargin an kulle su a ofishin 'yan sanda na Agugu dake garin Ibadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel