Sai da na shafe kwanaki 124 a hannun ’yan sanda a cikin 2018 – Dino Melaye

Sai da na shafe kwanaki 124 a hannun ’yan sanda a cikin 2018 – Dino Melaye

Sanata mai wakiltan yankin Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya bayyana cikin 2018 ya shafe tsawon kwanaki 124 a hannun jami’an ‘yan sanda daga arangamar su da dama da suka yi a cikin shekarar da ta gabata.

Sanatan ya ci gaba da cewa ranar da ‘yan daba suka kutsa kai cikin Majalisar Dattawa za ta kasance ranar da ta fi saura bakin ciki a shekaru hudu na zangon Majalisar Dattawa ta takwas da ya shude a wannan makon.

Melaye yayi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke jawabin bankwana da Majalisar Dattawa ta shirya a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni.

Dino ya soma jawabi ne ta hanyar jinjinawa Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Bukola Saraki bisa jajircewarsa wajen tabbatar da cewa bai zama wanda ake juyawa kamar waina ba.

Ya kuma tunatar da cewa ya sha bayyana Saraki a matsayin Shugaban Majalisar da ba a iya tsigewa, musamman lokacin da gwamnatin tarayya ta matsa masa lamba, har ta maka shi kara a Kotun CCT.

“Ni kai na a lokacin da Gwamnan Jihar Kogi ya shirya yi min kiranye, ai ina tsare a hannun jami’an ’yan sanda. Amma ga ni a yau ina mai godiya ga Ubangiji.

“A cikin 2017 an kama ni sau takwas. Cikin 2018 an damke ni sau 18, inda na shafe kwanaki 124 daga cikin kwanaki 365 na shekara daya.

“Kwana hudu kawai na samu na yi kamfen a zaben 2019, kuma na yi nasara. Don haka ba ni da wani dalilin da ba zan nuna godiya ta ga ubangiji ba. Gwamnatin Tarayya ta maka ni kotuna daban-daban.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da Hakimai 2 saboda rashin biyayya ga masarautar Rano

"Amma duk da haka sai da na sake dawowa Majalisar Dattawa a matsayin Sanata.”

Daga nan kuma ya kara da cewa ba zai amince ko ya bada goyon baya Majalisa ta zama a karkashin wasu ‘yan amshin Shatan shugabannin wata jam’iyya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel