Ka bawa masu bincike hadin kai - Yakasai ya fadawa Sarki Sanusi

Ka bawa masu bincike hadin kai - Yakasai ya fadawa Sarki Sanusi

Dattaijon dan siyasa, Alhaji Tanko Yakasai ya shawarci masu binciken zargin almundanar kudi a masarautar Kano su kasance masu gaskiya da adalci wurin gudanar da aikinsu.

A yayin da ya ke tsokaci kan takardan neman ba'asi da gwamnatin Kano ta aike wa Sarki Sanusi a ranar Alhamis, dattijon ya ce takardan neman ba'asin ba abin tayar da hankali bane ila wata hanya ce na gano gaskiya a cikin kowanne lamari.

Ya shawarci Sarkin ya yi nazarin dukkan zargin da ake masa ya kuma bayar da amsoshi inda ya ce abinda ya da ce shine idan ana zargin mutum da aikata wani abu sai a bashi ikon ya mayar da ba'asi ya kuma kare kansa.

DUBA WANNAN: Saraki ya bayyana ranar da tafi bakanta masa rai a majalisa

Alhaji Tanko ya ce ya karanta rahoton takardan neman ba'asin ne a kafar sada zumunta kuma cikin abinda ya tuna shine hukumar sauraron karar al'umma da yaki da rashawa na jihar Kano ta ce sarkin baya ba ta hadin kai wurin binciken.

Ya gargadi sarkin cewa rashin bayar da hadin kai ga masu binciken ba zai taimaka masa ba a yanzu tunda yin shiru ko kin amsa ba'asi na nufin rashin gaskiya ne a shari'ance.

Dattijon ya kara da cewa baya goyon bayan sarkin ya yi sauka daga karaga mulki a yanzu inda ya ce hakan bai zai magance matsalar ba domin za a cigaba da zarginsa ko bayan ya sauka daga mulki a matsayin sarkin Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel