Kotu ta wanke wata mata bayan zarginta da kisan kai

Kotu ta wanke wata mata bayan zarginta da kisan kai

- Babbar kotun Abuja ta wanke Amina Dauda daga zarginta da ake na kisan mijinta Muhammad Matazu

- Alkalin kotun mai suna Hussain Baba Yusuf ne ya wanke ta daga zargin bayan bangaren shigar da kara sun gagara gamsar da kotu da hujjoji masu karfi

Babbar kotu dake Maitama a Abuja ta wanke wata mata mai suna Amina Dauda daga zarginta da ake da kisan mijinta Muhammad Matazu tsohon ma’aikacin gidan rediyon kasa na FRCN Kaduna.

Amina Dauda mai shekaru 28, ta tsinci kanta gaban kotu bisa zarginta da ake na aikata laifin kisan mijinta a ranar 22 ga watan Mayun 2013. Alkalin dake jagorantar wannan shari’a shine Hussain Baba Yusuf inda kuwa laifin da ake tuhumarta da shi hukuncinsa kisa ne kamar yadda yake a sashe na 221.

Kamfanin dillacin labarai wato NAN sun ruwaito cewa wanda ya shigar da karar Amina ya ce ta yi amfani da fetur ne ta kona shi marigayin a gidansu dake shiyar Gwarimpa a Abuja.

Yayin da yake yanke hukunci kan wannan shari’a Jastis Hussain Baba Yusuf ya ce jami’an yan sanda basu binciken da ya dace ba kan wannan lamari.

KU KARANTA: Da zafinsa: Rabuwar kawuna tsakanin Gwamnoni yayin ganawa da Buhari

“Sam jami’an yan sanda ba suyi binciken da ya dace ba kan wannan lamarin. Dukkanin shaidu biyar da suka gabatar a gaban kotu babu ko guda wanda wannan abu ya auku a kan idonsa.

“Kada ku manta ita fa shari’a sabanin hankali ce. Hakika anyi kisan kai amma babu wanda aka kawo mana matsayin shaida wanda yana wurin akayi kisan.

“A dalilin hakan, la’akari da nuna rashin kwarewa daga wurin jami’an yan sanda a fannin gudanar da bincike kuma wacce ake zargin bata amsa laifin da ake tuhumarta da shi ba. A matsayina na wanda ke jagorantar wannan shari’a na wanke Amina Dauda daga zargi.” Inji alkalin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel